Kungiyar Amnesty International ta ruwaito cewa tun daga watan Janairu, mutanen Jebel Marra, suna ganin wasu irin kuraje suna fito musu a jiki, inda daga baya kuma fatar jikinsu ta kan zagwanye, sannan wasu suna fama da ciwon ido, wanda ke haddasa makanta da aman jini da gudawa da kuma matsalar yin numfashi.
Kungiyar ta Amnesty ta ce wadannan rashe-rashen lafiya, alama ce da ke nuna cewa hukumomin na Sudan sun yi amfani da sinadari mai guba.
Akalla mutane 250 ne suka mutu sanadiyar hakan kuma akwai yara da dama a cikinsu, sannan akwai wadanda suka jikkata da dama, in ji kungiyar ta Amnesty.
Sai dai a wata wasika da ya rubuta, ministan Shari’ar kasar ta Sudan, Awad Hassan Elnour, ya ce gwamnati ta cika da mamaki, da jin wannan ikrarin, yana mai cewa wata tawagar gwamnati ta kai ziyara a watan Fabrairu a yankin na Dafur, kuma babu wani da ya yi korafi dangane da wadannan alamun cututtuka.