Gwamnatin Nijar ta shirya taro na musamman na shugabannin jami’o’in kasar domin lalubo hanyoyin warware matsalolin da suka addabi jami’o’in da suka kawowa ci gaban ilimi mai zurfi cikas.
Ministan ilimi mai zurfi Yahuza Sadisu ya ce akwai cunkoson dalibai a ajin farko. Akan samu dubban dalibai na shekarar da ta gabata da basu samu wucewa gaba ba.
A cewarsa zasu yi tsari inda ajin farko za’a fara daga daya ga watan Satumba zuwa 31 ga watan Janairun sabuwar shekara. Cikin lokacin za’a bada karatu da jarabawa tare da bada sakamakon jarabawar. Za’a fara kashi na biyu na shekarar karatu daga daya ga watan Fabrairu zuwa 30 ga watan Yuni.
Taron wanda ke zama ci gaban wanda aka gudanar a watan Afirilun da ya gabata a Touha ya gano abubuwa da dama dake bukatar gyara inji shugaban jami’ar Touha Farfesa Ado Muhammad. Yace shekaru 47 da suka wuce Nijar nada jami’a daya kawai. A lokacin mutane miliyan uku ne kacal suke kasar. Yau tana da jami’o’i takwas da mutane miliyan 20 saboda haka yadda aka tafiyar da jami’a daya shekaru 47 da suka wuce ba zai zama daya ba da yadda ya kamata a gudanar da jami’o’i yanzu. Dole ne a zauna a yi tunane bisa bukatun kasar.
Tsarin gudanar da jami’o’in an gano yana bukatar sake dubawa. Dokokin tafiyar dasu suna bukatar waiwaya saboda a san nasarorin da aka samu, inda aka kasa da gyaran da ya dace a yi.
Farfesa Ado Muhammad yana ganin jin bahasin ministan ilimi mai zarfi alama ce cewa a wannan karon gwamnatin kasar da gaske take ta dauki matakan da suka dace domin gyaran lamuran jami’o’in kasar. Ya ce matsalolin jami’o’in ba na kudi ba ne kawai. Akwai matsalar ganewa.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum