Wannan matakin dai domin karfafa tsaro ne a wannan yankin da ‘yan bindiga ke kai komo a wani lokaci, musaman hana safarar makamai da miyagun kwayoyi da binciken mutanen dake shiga kasashen biyu.
A cewar Daraktar gundumar Iyakar Nijar da Najeriya ta Birni N'Konni na ‘yan sanda, Kwamishina Rabi'u Suley, duk kokarin da jami'an tsaro za suyi, shekar su ba zata cimma ruwa ba sai sun samu goyon bayan al'umma.
Ana sa bangaren daya daga cikin mukarraban da suka rakko tawagar hukumomin bariki da na gargajiya da ya halarci kaddamar da wannan wurin, yayi kira ga al'ummar Nijar da Najeriya da su rika kormatawa jami'an tsaro miyagun da ke kai komo a wannan iyakar, ko a cikin garuruwan su suke.
Tun dai lokacin da kasashen yammacin duniya suka hambarar da mulkin Kanar Ghaddafi, makaman kasar Lybia suka fada hannun 'yan ta'adda, asali ma, suka soma yawo a yankin Sahel, tare da haifar da hare-haren ‘yan bindiga, da ‘yan kishin Islama, da kuma masu garkuwa da mutane.
A cewar manazarcin lamuran tsaro a wannan yankin Jafaru Sarkin Shanu, wannan shirin, zai taimakawa kasashen Nijar da Najeriya a fannin tsaro .
Yanzu haka dai, jama'ar kasashen biyu suna soma sabawa da bin wannan wurin, yayin da masu yankewa suna bin daji duk da hakan ke haifar da shakku tsakanin su da jami'an tsaro dake saka na mujiya a wannan yankin.
Saurari cikakken rahoto daga Haruna Mamman Bako:
Dandalin Mu Tattauna