Yau a taron majalisar zartaswar tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin mukaddashin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo, gwamnati ta umurci mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Janar Muhammad Mongunu, da ya gudanar da cikakken bincike akan yunkurin raba Najeriya da wasu keyi.
Kwna kwanan nan 'yan kabilar Igbo suka tashi haikan suna neman su kafa tasu kasar da suka kira Biafra, sai kuma jiya wasu matasan arewa suka ba Igbo wa'adin watanni uku da su fice daga jihohin arewa su ma 'yan arewan dake kasar Igbo su koma gida a raba gari kowa ya kama tasa hanyar.
Wannan matsayin matasan arewacin Najeriya ya zo da bazata saboda shi ne karon farko da kungiyoyin suka hada kai har ma suka bada wa'adi cewa wata al'umma ta bar Najeriya yayinda suke ikirarin cewa 'yan arewa sun gaji da kasancewa cikin kasa daya da al'ummar Igbo.
Malam Garba Shehu kakakin fadar shugaban kasar Najeriya ya bada karin haske akan umurnin da gwamnati ta bada. Yana mai cewa maganar ta taso a taron majalisar ministoci. An lura cewa manyan maganganu suna fitowa daga bakin mutanen da ake cewa matasa ne. Sun nemi gwamnati tayi hattara domin kada a yi sakaci lamarin ya fi karfin kasar. Dalili ke nan da suka kira mai ba gwamnati shawara akan harkokin tsaro ya binciki lamarin domin a san matakin da za'a dauka.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum