Jawabin shugaban kasa Muhammad Buhari na mintuna hudu da 'yan kai ya taba zuciya da ratsa jiki matuka.
Shugaba Buhari ya tabo tattaunawar da ya yi da madugun 'yan tawayen Najeriya Odumegwu Ojukwu inda suka karkare a matsaya daya cewa abun da ya fi wa Najeriya a'ala shi ne ta cigaba da kasancewa kasa daya. Dole ne kasar Najeriya ta cigaba da dunkulewa kasa daya domin albarkatu da al'adu da Allah ya albarkaci kasar da su.
A jawabin Shugaban ya jawo hankalin jami'an tsaro cewa kada su bari nasarorin da aka samu a watanni goma sha takwas su tafi a haka kawai. Yakamata a sake salo tare da daura damarar yakar duk abubuwan da suka shafi harkokin ta'addanci.
Shugaba Buhari ya kira 'yan Najeriya da su sake damara wajen tunkarar duk abun da ya shafi Boko Haram da sauran ayyukan ta'addanci, kamar sace sacen mutane da rikicin manoma da makiyaya.
Yayi maganar abubuwan da suka shafi kabilanci da kuma uwa uba yadda baragurbin 'yan siyasa suke yiwa gwamnati batanci. A shirye gwamnati take ta danke ko ta yaki duk wani naui na ta'addanci da dan ta'adda na ciki da waje da wadanda suke fakewa da rigar siyasa da ta addini domin su cutar da al'umma.
Wajibi ne kasa tana kula da lafiya da dukiyoyin jama'a. A shirye gwamnati take domin tunkarar duk wani azzalumin da yake son cutar jama'a.
A saurari karin bayani a wannan:
Facebook Forum