Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Na Tattaunawa Da Boko Haram


 Lai Mohammed, ministan yada labaran Najeriya
Lai Mohammed, ministan yada labaran Najeriya

A wata sanarwa ta bakin ministan yada labaran Najeriya Lai Muhammad, a karon farko gwamnati tana tattaunawa da 'yan Boko Haram domin tsagaita wuta

Gwamnatin Najeriya ta ce tana tattaunawa da kungiyar Boko Haram a kan yiwuwar tsagaita wuta, kuma wannan tattaunawar tayi nisa, kamar yadda ministan yada labarai Lai Mohammed ya bayyana a jiya Lahadi.

Wannan shine karon farko a cikin shekaru da gwamnatin ta fito ta bayyana cewa tana magana da Boko Haram kan shirin tsagaita wuta. Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fada a baya cewa a shirye take ta gudanar da shawarwari da mayakan sakan, amma bata bada wani karin bayani ba.

Ahalinda ake ciki kuma, sama da yan mata dari da mayakan Boko Haram suka sako, sun koma ga hannun iyayensu jiya Lahadi.

A cikin watan Faburariru ne mayakan sakan suka yi garkuwa da yan matan da suka sace su daga garin Dapchi.


Bayan an sako ‘yan matan a ranar Laraba da ta gabata da kuma takaitacciyar ganawa da ‘yan matan suka yi da iyayensu cikin yanayi na tausayi, ‘yan makarantar sun kwashe kwanaki uku suna Abuja babban birnin kasar, inda suka gana da shugaba Muhammadu Buhari.


Shugaba Buhari yayi alkawari a ranar Juma’a cewa, zai yi iya bakin kokakrinsa ya tabbatar da an sako yarinya daya da ta rage hannun ‘yan Boko Haram mai suna Leah Sharibu wacce itace kadai kirista, kuma taki ta canza addininta.


Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG