Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Mulkin Sojin Misra ta yi Alkawarin Gudanar da Zaben Raba Gardama

Dan gwagwarmayar tabbatar da dimokaradiyya Wael Ghonim kenan a tsakiyar masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir.
Dan gwagwarmayar tabbatar da dimokaradiyya Wael Ghonim kenan a tsakiyar masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir.

Dan gwagwarmayar jaddada dimokaradiyyar nan na Misra, Wael Ghonim, ya ce sabbin shugabannin gwamnatin kasar ta mulkin soji, sun masa alkawarin gudanar da zaben raba gardama kan garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar a cikin watanni biyu.

Ghonim da wani mai sharhi ta internet sun buga wani bayani a dandalinsu na internet cewa sun sami wannan tabbacin a tattaunawarsu da Majalisar Sojojin da suka amshi ragamar iko daga Shugaba Hosni Mubarak bayan da ya yi murabus ranar Jumma’ar da ta gabata. Sun bayyana tattaunawar ta jiya Lahadi da cewa mai bayar da karfin gwiwa ce.

Ghonim, wanda wani babban jami’in kamfanin sadarwar internet din nan ne mai suna Google, das hi da wasu ‘yan gwagwarmaya masu amfani da kafar sadarwar internet, sun taka muhimmiyar rawa wajen shirya zanga-zangar gama gari ta kwanaki 18 ta kin gwamnati wadda ta tilasta wa Mubarak yin murabus da mika wa soji ragamar iko bayan shekaru 30 bisa gadon mulki.

‘Yan gwagwarmayar sun ce Majalisar Mulkin Sojin ta gaya masu cewa wani sabon kwamitin da za a kafa zai kammala rubuta gyare-gyaren kundin tsarin mulkin cikin kwanaki 10 kuma ta nemi amincewar jama’a ta gudanar da zaben raba gardama a fadin kasar cikin watanni biyu. Shugabannin gwamnatin mukin sojin na Misra ba sub a su tabbatar da wannan ba tukunna.

XS
SM
MD
LG