Gwamnatin Lebanon ta ayyana dokar ta baci ta tsawon makwanni biyu a yau Laraba a Beirut, kana ta umarci rundunar soji da ta yi daurin talala ga duk wanda ke da hannu a ajiye kayayyaki masu fashewa da suka tarwatse a tashar jiragen ruwan birnin, lamarin da ya shafi dukkan gine-ginen da ke kusa, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Dokar ta baiwa rundunar sojin cikakken iko bayan mummunar fashewar da ta auku a ranar Talata.
Har yanzu ba’a kai ga gano ainihin musabbabin fashewar ba, to amma jami’an kasar ta Lebanon suna ba da karfi ne akan abin da suka ce ton-ton na sinadarin ammonium nitrate da aka adana a tashar jiragen ruwan tsawon shekaru shida.
Fashe-fashen sun lalata daukacin gine-ginen da ke kusa, suka kuma kashe akalla mutane 135, tare da jikkata fiye da wasu dubu biyar, a cewar Ministan lafiya Hamad Hassan a yau Laraba.
Gwamnan Beirut Marwan Abboud, ya ce wannan mummunan ibtila’in ya kuma raba mutane kusan dubu dari uku da gidajensu.
Ma’aikatan ceto na ci gaba da binciken wadanda lamarin ya rutsa da su a yau Laraba, a yayin da Firai Minista Hassa Diab, ya ayyana zaman makoki na kwanaki 3 a fadin kasar.
Jami’ai sun ce suna sa ran adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ya karu, a daidai lokacin da ma’aikatan ceto ke ci gaba da binciken baraguzan gine-ginen da suka rushe, a yayin da sauran mutane ke ci gaba da neman ‘yan uwa da abokai da ba’a gani ba.
Baba Yakubu Makeri ya yi hira da Hudu Jasir Umar, wani dan asalin kasar Ghana da ke zaune inda lamari ya faru, ya kuma bayyana halin da a ke ciki.
saurari bayanin nasa.
Facebook Forum