A cikin wannan satin ne gwamnatin kasar Kenya ta tuhumi wasu manyan jami’an ta biyu da suke jin sun fi karfin doka.
Ana dai tuhumar wadannan jami’an ne da laifin cin hanci da rashawa na zunzurutun kudi har dala miliyan 3 na ginin hanyan jirgin kasar da wani kanfanin kasar China ke ginawa a kasar.
Wannan tuhumar na manyan jami’an wata manuniya ce ga gwamnatin Uhuru Kenyata cewa ba wani jami’in gwamnati da ya fi karfin doka a yakin da gwamnatin ke yi da cin hanci da rashawa.
Sai dai masu sharhi akan al’amurran yau da kullun suna cewa suna fata wannan tuhumar za ta kai ga gurfanar dasu har a kai ga yanke musu hukunci, wanda hakan zai zamo abin tarihi da gwamnatin ta Kenyata za ta bari ko kuma kila barazana ce irin ta ‘yan siyasa.
Wakilin Muryar Amurka dake aiko da rahoto daga Kenya Real Ombour ya ce babban darektan kanfanin jirgin kasa na kasar Atanas Maina da shugaban hukumar kula da albarkatun kasa Mohammed Swazuri, su ake tuhuma da laifin aringizon dala miliyan biyu na biyan kudin diyya.
Sai dai ko baya ga wadannan mutanen biyu haka kuma akwai sauran jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa da yawa dake fuskantar tuhuma da saye da sayar da filin gwamnati.
Facebook Forum