Duk da fitowar jihar inda ta musanta rahoton amma ta amince akwai rashin aikin yi wanda ta ce ruwan dare ne gama gari. Hakan ya sa jihar ta fito da sabbin tsare-tsare da karfafawa jama'a dogaro da kai ta hanyar koyar dasu sana'o'in hannu. Wannan shirin an yi ne domin mata da matasa musamman wadanda suka gama makaranta amma babu abun yi a karkashin ma'aikatar bunkasa alamuran mata.
Uwargidan gwamnan Katsina Hajiya Fatima Shema ita ce ta shugabanci bikin saukar karatu kashin farko na wadanda suka samu horo. Mata dari da hamsin aka horas dasu a kan sana'o'i daban daban kamar kwalliyar jiki da gyaran gashi da yin turare da gyara gidaje da yadda ake shirya bukukuwa da dai sauransu.
Wadanda aka horas sun samu kayan tallafi na soma sana'o'in da aka koya masu. Matar gwamnan ta ce akwai sana'o'i kanana wadanda sai an je makwaftan jihohi ake yinsu.Ta ce kullun ana biki da suna a jihar dalili ke nan suka tuntubi gwamna ya taimaka a koyawa mutane sana'o'in domin mutane su samu sana'ar yi a kuma rage zaman kashe wando domin a samu cigaba.
Wasu da suka anfana da horaswar sun fadi albarkacin bakinsu. Wata Fidelcis Yusuf da ta koyi yin kwalliya ta ce an bata kayan kwalliya da firigi wadanda zata fara sana'arta da su. Ta ce su masu karamin karfin sun ji dadin abun da aka yi masu. Ita na Hadiza Ibrahim wadda ta koyi dilka da yin turaren wuta ta ce an basu kayan aiki kuma ta ji dadi.
Ga karin bayani.