Biyo bayan wannan abun kunya da ya faru a makarantar ya sa gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike.
Kwamitin mai wakilai 14 na karkashin tsohon shugaban Jami'ar Maiduguri Farfasa Abubakar Mustapha. Gwamnati ta bashi makonni biyu ne kacal ya kammala aikinsa ya kuma mika mata rahoto.
Bayan kafofin yada labarai su ma kungiyoyin dake fafutikan kare yara sun ce zasu bada nasu gudummawar saboda tabbatar da gaskiya da adalci.
Malam Muhammad Ali Mashi shugaban wata kungiya mai gwagwarmayar kare yara da cin zarafi yace zasu nada kwamiti da zai bi kadun duk abubuwan da ake yi. Kwamitin nasu zai zauna da yaran da ma iyayensu da kuma wasu da ake zaton sun cutu ya yi bincike kan abun da ya faru. Zai kuma sa ido akan abun da kwamitin gwamnati zai zartas. Zasu dage sai an hukunta wanda ya kamata a hukunta kuma a ba mai gaskiya gaskiyarsa.
Tuni dai wasu iyayen daliban suka bada bahasi a gaban kwamitin. Sun bayyana wa kwamitin abubuwan da suka ji da can da sauran korafe korafe da suke dashi.
To saidai Barrister Audu Bulama lauya dake gwagwarmaya yace a fahimtarsa kafa kwamitin bata lokaci ne da kuma maimaita aiki saboda akwai kwamiti na musamman da gwamnatin tarayya ta kafa wanda yake da reshe a Kano. Aikinsa ne ya kare yara a duk fadin Najeriya.
Ga karin bayani.