Nufin kafa bankunan shi ne bunkasa harkokin noma da kananan sana'o'i a tsakanin al'ummar jihar.
Kawo yanzu dai wasu daga cikinsu na kokarin taka rawar gani ta fuskar nauyin da aka rataya masu amma duk da haka suna fuskantar dimbin kalubale kamar yadda guda daga cikin jagororin bankunan ya bayyana.
Yace akwai karancin jari da aka kafa bankunan. Kowane ya soma da jarin nera miliyan ashirin ne kamar yadda doka ta tanada. Kudin sun yi kadan. Mutane kuma basa son su yi huldar ajiye kudi a bankunan saidai an ce su zo su karbi bashi. Wannan yana dakile cigaban bankunan.
Wasu sun anfana. Sun sami karin jari. Sun bunkasa rayuwarsu kuma ta canza amma suna bukatar a sake kara masu kudi fiye da yadda aka basu. Akwai wani abu kuma. Su kansu mutanen akwai masu taurin kai. Bashi kawai suke son su karba kuma ba ashirye suke ba su maido da kudin.
Amma Farfasa Isa Dan Dago dake zaman sabon kwamishanan kudi na jihar yace akwai bukatar a yiwa bankunan garambawul ta hanyar canza masu suna da tsarin ayyukansu domin su yi daidai da na musulunci ko zasu samu karbuwa.
Yace banki na musulunci abu ne na hadin gwiwa tsakanin banki da mutum, ya kawo nashi kudin baki kuma ya kawo nashi. A hadu a yi mudaraba ko a yi musharaka ko a yi muraddana ko ijara wanda mutum zai san an bashi wata gudummawa ya bunkasa harakar kasuwancinshi. Shi ma bankin zai yi anfani da kai ya cimma muradunsa. Daga karshe ba'a maganar mai bada bashi da mai karbar bashi. Irin wannan a ke son a yi da kananan bankuna. A jawo kananan 'yan kasuwa wadanda jarinsu bai wuce dubu goma ko ashirin ba.
To amma sabuwar kwamishanar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki Hajiya Aisha Muhammad Bello na mai ra'ayin cewa bata ga laifin bankunan kasuwanci ba idan sun nemi a bayar da jingina kafin su bada bashi. Tace yanzu gaskiyar mutane ta yi rauni. Wani zai karbi kudi ba da niyyar biya ba. Amma idan ya san ya ba da jingina dole ya nemi hanyar biya.
Akan kananan'yan kasuwa wadanda jarin da suke nema bai wuce dubu ashirin ba Hajiya Aisha cewa ta yi a hadasu kamar kungiya kungiya ko cooperative a turance su karbi bashi. Idan mutane goma ke kungiya daya idan mutum daya bai iya biyan bashin da aka bashi ba sauran zasu yi karo-karo su biya. Saboda haka mutanen goman nan zasu hada kai su tabbatar sun yi abun da suka karbi kudi kansa. Su 'yan kungiyar zasu dinga sa idanu kansu da kansu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.