WASHINGTON, DC —
Wakilin Sashen Hausa a kasar Kamaru Mamadou Dandah ya aiko da rahoto a kan kokarin da hukumomin kasar Kamarun suka fara yi na kwashe 'yan kasar daga Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya wadda ke fama da rigingimu. Kamar yadda za ku ji a cikin rahoton na Mamadou Dandah, kafin ma gwamnatin kasar Kamaru ta kaddamar da kwashe 'yan kasar daga kasar Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya, daruruwan 'yan kasar Kamaru da ke zaune a Bangui babban birnin kasar sun tsallaka kan iyaka sun koma gida.
Gwamnatin Kamaru na Kwashe 'Yan Kasar Daga Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya

Rikicin kasar jamahuriyar Afirka ta Tsakiya na kora 'yan kasar Kamaru su na komawa gida