Shugabannin gwamnatin Kamaru sun rabtaba hannu kan yarjejeniyar da suka cimma da shugabannin bangaren masu anfani da harshen Ingilishi a kasar.
Mazauna bangaren na Ingilishi sun kwashe sama da watanni biyu suna artabu da gwamnatin kasar.
Shugaban kasar ta Kamaru shi ya tura wata tawaga da zummar shawo kan rikicin da yaki ci yaki cinyewa a bangaren Ingilishin. Rikicin ya rutsa da rayukan jama'a da dama lamarin da ya sa gwamnati ta jibge masu karin dakarun tsaro tare da yin yunkurin tilastawa yankin ya amince da muradun gwamnatin kasar.
Malam Balarabe Musa wanda yake cikin kwamitin na gwamnati yace an samu an zauna da bangaren Ingilishin an kuma tattauna dasu. Yace yanzu ana iya cewa kusan komi ya koma daidai saboda su shugabannin sun sa hannu a takardar yarjejeniyar da aka yi dasu.
Yanzu an yadda lauyoyi su koma bakin aiki. Kasuwanni kuma a budesu kana 'yan makaranta su koma bakin karatu. Amma akan komawa makaranta an dan samu tsaiko domin masu koyon Ingilishi daga bangaren Faransanci ne suka koma.
Malam Abubakar daya daga cikin masu fada a ji a bangaren Ingilishi yace basu yadda zasu koma bakin aikinsu ba. Takardar da suka sawa hannu can tsakaninsu ne inji Abubakar. Amma su sai gwamnati ta yadda ta basu hakkinsu zasu koma kana yara ma su koma makaranta.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.