Gwamnatin jihar Neja ta ce zata ciwo bashin Nera miliyan dubu ishirin da daya da miliyan dari biyar, domin gudanar da wasu ayyukan raya kasa a jihar.
Amma babbar jam'iyyar adawa wato PDP ta nuna rashin gamsuwa da dalila ciwo bashin.
A wani taron manema labarai da kwamishanan kudi na jihar Alhaji Zakari Abubakar ya kira, ya ce zasu karbo bashin ne a karkashin shirin nan na Sukuk wanda bashi da ruwa.
A karin bayanin da ya yi, kwamishanan ya ce da farko za'a karbi Naira biliyan goma sha biyu da miliyan dari biyar cikin wannan shekarar. Sannan badi sai su nemi sauran biliyan tara a cewarsa. Ya kara da cewa suna bukatan bashin ne domin aiwatar da ayyukan da zasu kara karfafa arzikin kasa.
Akan ayyukan da zasu yi kwamishanan ya ce akwai gyaran asibitin Kontagora da batun gyaran ma'adanan kasa.
Amma jam'iyyar PDP tana shakkun dalilan da gwamnatin ta bayar na ciwo bashin a dai dai wannan lokaci.Barrister Tanko Beji, shugaban jam'iyyar a jihar ya ce a gaya masu abubuwan da za'a yi da kudaden, sannan yana shakku ko majalisa ta ba gwamnati daman ciwo bashin. Ya bukaci a kuma bayyana ayyukan da aka yi da basusukan bayan da aka ciwo.
Majalisar dokokin jihar ta tabbatar da sanin batun ciwo bashin, saboda Gwamnan jihar ya sanarda ita inji shugaban kwamitin labarai na majalisar Sha'aibu Liman Iya.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum