Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Borno Ta Nemo Tallafin China


Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno yana dubar barnar da aka yi a Baga kwanakin baya
Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno yana dubar barnar da aka yi a Baga kwanakin baya

Gwamna Kashim Shettima ya gayyato kwararru domin kafa masana'antu da koyar da matasan Jihar wasu sana'o'i, yayin da za a tura wasu zuwa China.

A wani yunkurin samarwa da matasa aiki domin dakile tashin hankalin da ake fama da shi a jihar Borno, gwamna Kashim Shettima yayi tattaki har zuwa kasar China, inda ya gayyato wasu kwararru domin su zo su taimaka musu wajen kakkafa masana'antu sarrafa amfanin gonar da ake nomawa a jihar.

Daga cikin abubuwan da wadannan kwararru na kasar China zasu taimaka wajen kakkafawa, har da masana'antun sarrafa tumatur, da barkono da wasu kayan danye, maimakon a rika fita kasashen waje da wadannan kayayyaki ana sarrafa musu, sannan a komo da shi ana sayarwa da tsada.

A bayan kuma da aka kashe wani dan kasar China mai aikin kwangila kwanakin baya a jihar ta Borno, 'yan kasar duk sun wkashe kayayyakinsu sun gudu. Yanzu kamfanin dake wannan aikin, ya yarda cewa za a tura matasa 'yan jihar Borno wadanda suke da takardun kammala karatunsu a aikin injiniya ko gini ko makamancin hakan, zuwa kasar China domin kamfanin ya koya musu dukkan matakan irin wannan aiki, su komo su na gudanarwa da kansu a jihar.

Makasudin wadannan ayyuka dai shi ne rage yawan matasan dake zaune babu aikin yi, domin hana su shiga ko fadawa cikin tarkon tsagera da zasu nemi yin amfani da su domin kawo tashin hankali.

Haruna Dauda ya aiko da karin bayani kan wannan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG