Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Borno Ta Jaddada Muhimmancin Hana Wayar Salalu


An koma 'yar gidan jiya a jihar Borno ta yadda sai an tafi kusa da kan iyakar wasu jihohi ake iya wayar salula.
An koma 'yar gidan jiya a jihar Borno ta yadda sai an tafi kusa da kan iyakar wasu jihohi ake iya wayar salula.

Gwamnatin jihar Borno ta arewa maso gabashin Nijeriya ta kare cigaba da katse wayar salalu da ake yi a jihar, duk kuwa da maido da layukan a sauran jihohin.

Yayin da wasu ke alakanta munanan hare-haren da aka gani kwanan nan a arewa maso gabashin Nijeriya da birnin Kano da daina katse layukan salula da aka yi a sassan arewa maso gabashin Nijeriya, gwamnatin jihar Borno ta arewa maso gabashin kasar ta kare cigaba da katse layukan wayoyin salula da ta ke yi duk kuwa da maido da layukan a makwabtan jihohi.

Da ya ke bayani ga wakilinmu na jihar Borno Haruna Dauda Biu, bayan ganawa da wata tawagar Kwamitin Majalisar Dattawan Nijeriya kan Batun Tsaro da ke ziyara a jihar, Mataimakin Gwamnan jihar ta Borno Alhaji Zannan Umar Mustapha ya ce ba shakka wayar salula na taimakawa wajen kai hare-haren da ake yi a jihar, kuma sun ga fa'idar katse wayar. Ya ce jihar Borno ce ta fi fama da munanan hare-haren da aka yi ta kaiwa, don haka sun gwammace rashin aiki da wayar salula da rashin kwanciyar hankalin da wayar ke janyo masu.

Kwamitin Majalisar Dattawan ya kai ziyara jihar ta Borno ce don gane wa kansa cigaban da aka samu ko akasin haka da kuma irin korafi ko shawarar da jama'a da hukumomin da abin ya shafa ka bayar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG