Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya ce zai gurfanar da tsofaffin gwamnonin jihar guda biyu gaban hukuma, ciki har da Malam Isa Yuguda da kuma Barrister Mohammed Abdullahi Abubakar, saboda da yin sama da fadi da kudade fiye da Tiriliyan daya, wato naira Biliyan dubu na gwamnatin jihar Bauchi da suka yi a zamanin mulkinsu.
Kwamitin da gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya kafa domin ya karbo kudade da kadarorin da gwamnatocin Malam Isa Yuguda da kuma Barrister Mohammed Abdullahi Abubakar suka salwantar, ya bukaci su mai da kudaden.
Bugu da kari kwamitin ya ce akwai wasu filaye a jihar Kaduna da kuma wasu gidaje a garin Kano da ya gano mallakar jihar Bauchi da ake kokarin salwantar da su.
Sai dai mai ba tsohon gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar shawara a fannin labarai, Ali M. Ali, ya ce wannan zancen tamkar tatsuniya ce. Ya kara da cewa wadannan zarge-zargen ana wasa da hankalin mutanan jihar Bauchi ne kawai.
A jawabinsa, gwamna Bala Muhammed, ya yaba wa mambobin kwamitin dangane da kokarinsu na bankado irin almundahana da sama da fadi da aka yi da kudaden jihar, ya kuma yi alkawarin gabatar da duk wanda aka samu da laifi gaban shari’a domin a hukunta su.
Ga karin bayani cikin sauti.