Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Za Ta Kara Mayar Da Hankali Kan Harkar Man Fetur Da Zinari


DR Mahmud Bawumia Mataimakin Shugaban Kasar Ghana
DR Mahmud Bawumia Mataimakin Shugaban Kasar Ghana

Gwamnatin Ghana ta sanar da matakin sayen man fetur da gwal maimakon amfani da kudaden waje. Wannan wani mataki ne da gwamnatin ta ce bayan tallafin IMF zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar da ya fadi warwas.

Mataimakin shugaban Ghana Dakta Mahmud Bawumia ne ya bayyana hakan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar makamashi a Ghana, inda yake cewa "bayan tallafin asusun lamuni na IMF, ya kamata kasar ta nemi wasu hanyoyi da zata magance matsalolinta. Idan tsarin ya fara aiki, zai rage abin da ake kashewa, sannan zai rage ci gaban faduwar darajar kudin kasar da ake alakantawa da tashin farashin mai, a cewarsa.

Shugaban babban bankin kasar na Bank Of Ghana Dakta Ernest Addison, ya fada wa manema labarai bayan tsokacin mataimakin shugaban cewa manya-manyan kamfanonin hakar ma'adinai a Ghana na fitar da gwal da ya kai dalar Amurka biliyan uku a kowace shekara, don haka gwamnati zata rinka sayen kashi ashirin cikin dari na gwal daga garesu daga shekara mai zuwa.

Mai sharhi kan harkar makamashi a Ghana, kuma malami a jami'ar kimiyya da fasaha ta KNUST da ke Kumasi Dakta Kwame, yace wannan mataki ya taimaka musamman a wannan lokaci da kasar ke fama da tsadar man fetur, amma kuma matakin ba zai dawwama ba.

Dakta Kwame Sarkodie na ganin kamata yayi gwamnati ta maida hankali wajen farfadoda da babbar matatar mai ta kasa wato Tema Oil refinery, abinda yace hakan zai sa Ghana dogaro da kai wajen amfani da man fetir saboda kasar na hakar danyen mai cikin gida.

Shi kuwa mai sharhi kan harkar hakar ma'adinai ta kasa wato Baba Muhammad na ganin wannan mataki da gwamnati ta dauka yayi daidai tare da bai wa gwamnati shawarar cewa tayi kokarin farfado da matatar mai ta kasa ko da rance zata karba maimakon ta dukufa kan musayar man fetur da gwal.

Ana dai sa ran cewa tsarin zai fara aiki a karshen watanni uku na farkon shekarar 2023.

Saurari rahoton Hamza Adam:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG