Barrister Kaka Shehu Lawan shi ne shugaban kwamitin dake raba gidajen da gwamnati ta ginawa al'umma.Yace tun kafin ta'asar 'yan Boko Haram gwamnan jihar Kashim Shettima ya shirya gina gidaje dubu dari biyu wa wadanda suke zaune cikin gidajen kara.
Sun fara ginin a Mafa sai 'yan Boko Haram suka farma wurin. Mutanen wurin su ne na farko da 'yan Boko Haram suka rabasu da muhallansu suka zauna ciki suna abubuwan da basu dace ba. Daga bisani aka sa sojoji suka rusa wurin domin tarwatsa 'yan Boko Haram daga wurin.
Neman zaman lafiya yasa gwamnati ta rusa gidajen amma tayi aniyar gina masu wasu domin ba laifinsu ba ne. Masifa ce Allah ya kawo. Duk garuruwan da 'yan Boko Haram suka kone gidaje idan zaman lafiya ya dawo walau gwamnati ta ginawa mutanen gidaje ko ta gyara masu.
Mutanen da suka anfana da wannan yunkurin na gwamnati sun yaba da abun da aka yi masu. Wasunsu basu yi tsammanin zasu sake samun gidaje ba. Sun yiwa Allah godiya da kuma gwamnatin da ta taimaka masu.
Ga rahoton Ibrahim Dauda Biu.
Haruna Dauda Biu