Malam Yakubu Ibn Muhammad mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi akan harkokin labarai ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan zargin da su keyi na cewa gwamnatin da ta shude ta yi facaka da nera biliyan casa'in da daya d sunan tsaro cikin shekaru takwas.
Daga shekarar 2007 zuwa ta 2015 gwamnatin da ta shude ta kashe wasu kudade da sunan harkokin tsaro ckin shekaru takwas..
Malam Muhammad yace manufarsu ita ce su nunawa jama'a irin kudaden da aka kashe da sunan samarda tsaro.
A cewar Yakubu Ibn Muhammad gwamnan jihar na yanzu ya rantse duk kudin da aka kashe akan hanyar da bata dace ba to sai an dawo dasu. Gwamnatin zata bi duk hanyoyin da suka wajaba domin a samo kudaden.
Alhaji Salisu Tafawa Balewa wani tsohon kwamishana a gwamnatin da ta shude yace duk kudin da tsohuwar gwamnati ta kashe sai da ta sami amincewar majalisa. Yace kamata ya yi jama'ar jihar su gane cewa kare rayukan jama'a da lafiyarsu da dukiyoyinsu abubuwa ne da suka rataya a wuyan gwamna. Idana aka yi la'akari da irin zaman lafiyar da jihar ta samu da kuma abubuwan dake faruwa a jihohi dake mkwaftaka da ita batun kashe kudi akan harkokin tsaro ba wani abu ba ne da za'a cigaba da yin ccekuce akai.
Ga karin bayani.