YAOUNDÉ, CAMEROON- A kasar Kamaru gwamnati ta rugurgusa gidajen mutane da dama a wasu anguwanni da nufin gina babban Otel.
Hakan ya jawo tashin hankali, musamman ga mazauna unguwar Bali-Dikolo a Douala birnin cinikayyar Kasar.
A makon da ya gabata gwamnati ta rusa gidajensu a karamar hukumar Douala na daya.
Wadannan mutane sun wayi gari cikin lamari na tashin hankali, bayan da wani kamfani mai zaman kansa ya ce ya samu izini daga gwamnati ya afkawa gidajen da nufin gina wani babban Otel.
A wani taron manema labarai, Barrista Jeanne Msoga daya daga cikin wadanda suka rasa gidajen su ta ce firaminista ya yarda da ma’aikatansa shi ya sa yake amincewa da duk labarai da suke kai mishi.
Sarkin Doualawa mai martaba Jean Yves Eboumbou Douala Manga Bell ya ce “mun yi zama kusan sau goma sha biyar tun da aka fara wannan maganar.
Ya kara da cewa, "mun tattauna da Firaminista, da ministotin filaye da na shari’a, da Gwamnan Jihar Littoral domin kiyaye wannan rushe rushe, duba da kurakurai da ma’aikatan gwamnati suka yi a lokacin da suka fara bibiyar al’ummar mu don sanar dasu wannan aiki. Har majalisa a Yaounde mun aika sakonnin mu domin gudun abinda zai iya biyowa baya. Wannan daidai ya ke da kisan kare dangi na al'adu”
Al'ummar anguwar Japoma da ke karamar hukumar Douala na uku su ma suna cikin fargaba.
Sun fito kan titi domin nuna bacin ransu kan labarin da suka samu na rusa gidajensu a karshen wannan makon da muke ciki. Dauke da alluna da suka rubata cewa “ba za a dake mu kuma a hana mu kuka”
Wannan labarin rushe-rushen anguwanni ya mamaye kasar kamaru gaba daya. A nan Yaounde mun nemi karin haske daga bakin masu fada aji a ma’aikatan ministan filaye, amma an rufe mana kofa ba mu samu shiga ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mohamed Bachir Ladan: