Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Mayar Da Martani Kan Bukatar Majalisa Na Shugabannin Tsaro Su Yi Murabus


Sanata Ali Ndume
Sanata Ali Ndume

Bayan da majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugabbanin tsaro su ajiye mukamansu, gwamnatin kasar ta mayar da martani kan batun.

A cikin wata sanarwar da gwamnatin ta fitar mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, gwamnatin ta ce yin hakan aikinta ne.

"Sauke hafsoshin tsaro a Najeriya, abu ne da ke karkashin ikon gwamnati. Saboda haka shugaba Buhari zai yi abin da zai fi dacewa da Najeriya a yanzu.

Yunkurin na 'yan majalisar dokokin ya biyo bayan kashe-kashen sojojin da ke yaki da 'yan ta'addanci da ake yi a arewacin Najeriya.

Sanata Ali Ndume wanda ya kasance shugaban kwamitin soji na majalisar ne ya gabatar da kudurin a zauren majalisar.

Sauran sanatocin da su ka goyi bayan kudurin sun bayyana yadda lamarin ke matukar tayar musu da hankali.

A cewarsu, "wannan lamarin zai iya haddasa cikas a kokarin da ake yi na dakile 'yan bindigar."

Sun kuma jaddada yadda sojoji da dama wadanda ke tsoron rasa rayukansu suka fara ajiye mukamansu.

A jiya Litinin, babban hafsan hafsoshin Najeriya Tukur Buratai ya sheda wa manema labarai a birnin Abuja cewa kawo karshen ta'addanci na hannun 'yan Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG