Jihar Zamfara ita ce jihar da cutar sankarau ta fi addaba a cikin jihohin arewacin Najeriya lamarin da ya kaiga kafa sansanonin kula da wadanda suka kamu da cutar domin kula dasu da rage mutuwa.
Gwamnan jihar ya ziyarci sansanin da aka bude a Kauran Namoda domin gani da ido halin da masu jinya ke ciki. A lokacin ziyarar yayi kacibi da abun da bai yi tsamnanin zai faru ba.
Gwamnatinsa ta samar da maganin rigakafi da magugunan wakar da cutar da yakamata a ba mutane kyauta. Amma abun mamaki talakawan da aka samar ma magungunan sai gashi ma'aikatan kiwon lafiya na rubuta masu magungunan su je su saya da kudadensu. Duk wadanda gwamnan ya zanta dasu ya kuma ga magungunan a hanunsu sun nuna masa takardunsu kuma dukansu saya suka yi da kudadensu.
Gwamnan yana ganin almundahanar wata yunkuri ce ta yiwa kokarin gwamnatinsa zagon kasa bisa ga fafutikar da ake yi na yaki da cutar. Gwamnan yana mai cewa "mutum yana gap da zuwa lahira sannan a ce an baka abu dominsa sannan kayi son zuciya"
Dangane da wuraren da masu cutar suke zama gwamnan yace bai gamsu da wuraren ba. Bai gamsu da tsarin ba kwata kwata saboda haka ya bada umurnin a samar masu da wuri ingantacce tare da magunguna ingantattu.
Dangane da sayar da magungunan gwamnan yace bayan bincike dole ne a hukumta duk wanda aka samu da hannu cikin almundahanan.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Facebook Forum