Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Plato Ya Ce Zaman Lafiya Ya Dawo Jihar


Gwamnan Plato Simon Lalong da Shugaban Nigeria Muhammad Buhari
Gwamnan Plato Simon Lalong da Shugaban Nigeria Muhammad Buhari

Gwamnan jihar Plato Simon Lalong yace, a saboda matakan da gwamnatin sa ta dauka tare da taimakon gwamnatin taraiyar, yanzu zaman lafiya ya dawo a jihar sa.

Gwamnan Plato, Simon Lalong, ya ce yana wurin zaben shugabannin jam’iyyarsa na kasa ya ji labarin kashe kashe ya barke a jiharsa. Nan take ya nemi komawa jiharsa.

Jihar ta yi shekara uku a karkashin shugabancinsa ba’a samu tashin hankali ba sai wannan shekarar sabili da rikicin da ya barke tsakanin kabilun Berom da Fulani.

Yace yanzu sun shirya domin su tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar. Gwamnan yace babu ruwansa da batun addini ko kabilanci saboda ya taso a gidansu inda rabi Musulmi ne rabi kuma Kirista amma duka ‘yanuwan juna ne. Baicin hakan addinisa ma ya koya masa bashi da ikon daukan fansa kan wani.

Gwamna Lalong y ace babu dalilin samar da wasu hanyoyi dabam da mutane zasu bi zuwa jihohin arewa maso gabashi, maimakon bi ta birnin Jos kamar yadda wasu suka bukaci ayi, domin a matsayinsa na gwamna ya dauki matakan tabbatar da zaman lafiya..

A saurari cikakken bayani a wannan rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:05 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG