WASHINGTON, DC —
Bayan ya share kusan shekara daya ba ya gida, yana kwance a assibitocin kasashen Amurka da Jamus, gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai na shirin komawa gida a ranar Assabar din nan mai zuwa. Gwamnan ya dade yana jinya daga raunukkan da ya samu bayanda jirgin saman da yake tuki da kansa ya fado kasa a watan Oktobar da ya wuce. Aliyu Mustaphan Sokoto ya zanta da sakataren watsa labaran gwamnan, Hassan Mijinyawa kan aiyukkan da gwamnan zai soma bayan ya dawo:
Gwamnan Jihar Taraba Zai Koma Gida Karshen Makon Nan
- Aliyu Mustapha

Gwamnan jihar Taraba dake arewa-maso-gabashin Nigeria da ya dade kwance a assibitocin Turai zai koma gida karshen makon nan