Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya bukaci gwamnatin tarayya ta taikawa jiharsa saboda wadanda rigingimu suka rutsa dasu.
A wani taron ganawa da 'yan jaridu dake jihar gwamnan ya yaba masu da taimakon da suke baiwa gwamnati wajen cimma manufofinta. Ya kara da yi masu alkawarin basu bayanai da zasu bayyanawa jama'a saboda samun fahimtar juna.
Gwamnan yace tallafawa wadanda rigingimun jihar suka daidaita kamar yadda ake yiwa wadanda rigingimun Boko Haram suka rutsa dasu a arewa maso gabashin kasar zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.
Yace idan aka sake ginawa mutum gidansa da aka kone zuciyarsa zata kwanta. Haka ma idan aka samu kudi aka sayawa mutane shanu zasu samu karfin gwiwa, zuciya kuma ta kwanta..
Kwamitin da suka kafa na kawo sulhu ya bada umurnin a tallafawa mutanen da rigingimun suka shafa. Yace an kone gonakai tare da kashe shanu sabili da haka a yiwa mutanen abun da ake yiwa na arewa maso gabas.
Dangane da kudaden da suka yi batan dabo a gwamnatin da ta shude gwamnan yace suna kan bin sawu. Sun rubutawa EFCCda sunayen mutanen da ake kyautata zato sun san wani abu akan kudin.
Jihar ta dauki kamfanoni biyu da zasu yi masu binciken kwa kwaf a duk fadin jihar. Ya kira duk wanda ya san ya wawure kudin gwamnati ya dawo dasu.
Ga rahoton Zainab Babaji.