Gwamnan ya kira 'yan asalin Dikwa malaman makaranta dake aiki a yankin kafin rikicin Boko Haram da ma'aikatan kiwon lafiya da su kuka da kansu idan basu koma bakin aikinsu ba su taimaki jama'arsu.
Gwamnan yace gudummawar da zasu iya bayarwa ke nan ga mutanen dake zaune a sansanin 'yan gudun hijira kafin a sake gina masu muhallansu da wuraren more rayuwa. Kin bada tasu gudummawar zai gamu da fushin gwamnatinsa.
Garin Dikwa na cikin garuruwan da 'yan Boko Haram suka mamaye can baya kafin sojojin Najeriya su fatattakesu.
Tun lokacin da aka kwato garin da kauyukan dake kewaye dashi rundunar sojojin Najeriya ta kubutar da mutane da dama wadanda aka kafa masu sansanoni a cikin garin Dikwan.
A karshen makon da ya gabata ne kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa saboda tallafawa mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita ya ziyarci garin na Dikwa inda kwamitin da gwamnatin Borno suka rabtaba hannu akan shirin soma aikin sake gina garin.
'Yan gudun hijiran dake Dikwa yanzu sun fito ne daga kananan hukumomi guda shida kuma suna da bukatu da dama. Bukatunsu sun hada da ruwan sha, da muhallalai da asibitoci da sauran ababen more rayuwa.
Ga karin bayani