Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya zargi gwamnonin PDP da su ka canja sheka da yin butulci ma jam’iyyar tasu. Gwamna Lamido, wanda ke jawabi inda Shugaban kasa Mr. Goodluck Jonathan yak e yakin nema sake zabarsa a Sakkwato, y ace PDP ce ta dada fitar da gwamnonin a siyasance.
Wakilinmu a Sakkwato Murtala Faruk Sanyinna, wanda ya aiko da wannan rahoton, ya ruwaito gwamna Lamidon na cewa, “An zabi Wamakko, an kai kararsa, aka soke zabe mu ka zo wannan wuri – wurin PDP, wadda ake kira jam’iyyar azzalumai, ta masu kama karya; wannan jam’iyyar ta yi amfani da kama karya ya zauna a wannan matsayi nasa; a lokacinsu an yi kama karya an saka su. Idan kama karya aibi ne, ai an kama an karya an ba su.”
Wannan zargi na Sule Lamido dai yi ma ‘yan jam’iyyar APC dadi ba, don haka , a wani taron manema labarai da su ka kira, ‘yan jam’iyyar ta APC sun ce zargin da Sule Lamido shure-shure ne kawai. Dr. Muhammad Abubakar Sakkwato, daya daga cikin manyan magabatan APC a hijar Sakkwato a wurin taron, y ace, “Ina ganin wadannan da Sule Lamido ya yi, shi ya kamata ya zama mutum na karshe da zai yi su. Dalili kuwa, tafiyar nan da shi aka fara ta. To amma ana tsakar yinta, sai rikici ya taso na maganar dansa da aka kama da rashin gaskiya, don haka sai ya zama dole ya koma cikin wadancan da ke kare marasa gaskiya, in har kare marasa gaskiya ne aikinsu. Saboda haka ya taho y ace wani ya yi butulci, bag are shi ya kamata wannan maganar ta taso ba. Ga shi an gan shi cikin kazanta dumudumu, sannan kuma ya zo ya ce wani ya yi butulci – an kare mai an masa kaza – shi ai saboda a kare masa rashin gaskiyar shi ya sa ya koma. Ai shi ya yi butulci, shi da aka kama da rashin gaskiya.”
Dr. Muhammad Abubakar Sakkwato y ace su Sule Lamido na tsaron barin PDP saboda gudun abin da zai biyu baya. Y ace Wamakko ya daure saboda komai za a yi to a yi cikin gaskiya don amfanar jama’a.