Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana dalilin da yasa ya yanke shawarar sanya ‘yan wasa a cikin fili ba tare da la’akari da ‘yan wasan da suka kamata ba, a wasansu na cin kofin Zakarun Turai da Real Madrid a daren Laraba.
Kocin ya ajiye babban dan wasansa, Sergio Aguero, a benci, yayin da Gabriel Jesus kuwa ya buga bangaren hagu.
Dan wasan na kasar Brazil ya tayarwa da kungiyar Real Madrid hankali sosai, yayin da ya ci gaba da taimakawa kungiyar tana kare kanta.
Da yake magana bayan wasan, Guardiola ya ce: "Mun yanke shawarar yin wasa ba tare da babban dan wasan gaba ba, saboda yadda kungiyar ta Madrid ta ke kare gidanta.”
Ya kara da cewa, “Dole ka fadada wasanka, abokan karawar mu kuwa sun shigowa da karfin su, wanda hakan yasa mintuna kadan da fara wasan mun wahala, amma daga bisani mun samu nutsuwa.”
Facebook Forum