Daga cikin batutuwa da muka gabatar a wannan shirin cikin wannan shekara ta dubu biyu da goma sha takwas dake shigewa, akwai wannan batu na gallazawa abokan zama da take hakkokinsu wanda galibi yafi shafar mata da kananan yara.
Shirin Domin Iyali ya gayyaci masana da majibantan wannan lamarin domin neman gano masababin wannan lamarin da kuma matakan shawo kanshi.
Mun kuma kawo maku labarin wata karamar yarinya da aka yiwa fyade a sansanin ‘yan gudun hijira na Karmajiji dake Abuja.
Wani batu kuma da ya dauki hankalin shirin Domin Iyali a wannan shekarar shine sace ‘yammatan sakandaren Dapchi ranar goma sha tara ga watan Fabrairu kasa da watanni biyu kafin cika shekaru shekaru hudu da sace ‘yammatan Chibok.
Makonni biyu bayan gabatar da wannan shirin kungiyar Boko Haram ta saki dari da hudu daga cikin ‘yammata dari da goma da ta sace. Aka bayyana cewa, biyar sun mutu a kan hanya lokacin da aka yi garkuwa dasu yayinda kungiyar taki sakin daliba daya, Leah Sharibu wadda har yanzu take hannun kungiyar sabili da taki Musulunta.
A cikin watan Uku ne kuma wadansu ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Fredricah Wilson suka gayyaci wadansu ‘yammata da kungiyar Boko Haram tayi garkuwa dasu a garin Bama, wadanda cikin ikon Allah suka samu suka gudu.
Saurari shirin domin jin Karin bayani.
Facebook Forum