Yau shirin Domin Iyali zai sake bibiya kan wani batu da muka sha haska fitila a kai sai dai ganin hakar shirin bata cimma ruwa ba, yasa shirin ga ya dace a daidai wannan lokacin a sake jan hankalin masu ruwa da tsaki da suka hada da kusoshin siyasa, masu fada a ji, da sauran masu kada kuria. Batun da ake Magana a kai shine, batun damawa da mata a harkokin siyasa.
Wani matsayi da ba a jayayya a kai shine, cewa, kuri’un mata suna da matukar tasiri a nasarar kowanne dan siyasa, ko kuma jam’iya, ba a kasashen nahiyar Afrika kadai ba, har ma a sauran kasashen duniya. Sai dai duk da tasirinsu, bai kaisu ga mata samun cimma gurinsu na ganin an dama dasu a harkokin siyasa yadda ya kamata ba, duk da alkawuran da jam’iyun siyasa suke yi gabanin zabe.
Ganin an fara kada gangar zabe a Najeriya da kuma matakan da jam’iyun siyasa suka fara dauka na jan ra’ayi da neman goyon bayan mata, ya sa shirin Domin Iyali sake bibiya kan wannan batun.
Wakilin Sashen Hausa a birnin Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranci wani zaman tattaunawa na musamman domin neman matakan da za a iya dauka na daban da zai kai ga cimma wannan burin.
Saurari cikakken shirin.
Facebook Forum