WASHINGTON, DC —
A kashi uku kumam na karshe na hirarmu da Dr Rebecca Samuel Dali wadda ta sami lambar yabon yabo ta Sergio Viera de Mello, da MDD ke badawa bayan kowacce shekara biyu domin yabawa wadanda suka taka rawar gani a fannin ayyukan jinkai, musamman aikinta tsakanin wadanda harin kungiyar Boko Haram ya shafa, ta bayyana mani kalubalai da cibiyar ke fuskanta a gudanar da ayyukanta.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.