Idan kuna biye damu makon jiya, shirin Domin Iyali ya kawo maku rahoto na musamman kan batun aurar da 'yaya mata da wuri a Jamhuriyar Nijar inda bincike ya nuna, ana aurar da kashi saba'in cikin dari na 'ya'ya mata a kasar kafin su cika shekaru goma sha takwas. Kamar yadda muka alkawarta, yau shirin ya hada kan masu ruwa da tsaki domin gano inda wannan dabi'a ta sami asali da kuma matakan da za a iya dauka na shawo kanta. Yau ma shirin yana tare da Usman Ahmadu darektan ma'aikatar kula da kananan yara, da Madam Kako barma shugabar hadakar kungiyar mata a Niger, da kuma Lawali Adamu jami'in kungiyoyin farar hula Ga Wakilinmu Yusuf Abddullahi da ya jagoranci wannan tattaunawa.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.