WASHINGTON, DC —
A kashi hudu kuma na karshe a wannan bibiya kan batun ba mata kashi talatin da biyar cikin dari na madafun iko, bakin da muka gayyata domin musayar miyau, Hajiya Hauwa El-yakub wadda ta tsaya takarar wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattijan tarrayar Najeriya sai dai hakarta bata cimma ruwa ba, da kuma barrista A'isha Ali Tijjani yar gwaggarmayar kare hakkokin bil'adama musamman mata, sun bayyana abinda suke gani ya kamata gwamnati ta maida hankali a kai wajen cike guraba da kuma tabbatar da shugabancin kwarai .
Saurari cikakken shirin
Facebook Forum