WASHINGTON D.C. —
Kamfanin Google ya bayyana cewa yana gwajin sabuwar manhajar tsaro ta Google Maps wato (Taswirar duniya) da zata sanar da kai idan motarka ko tasi ta sauka daga kan hanyarka da zarar kayi tafiyar kimanin mita 500 ba akan hanya ba.
Manhajar da aka fara ganinta daga kamfanin XDA Developers, kuma ya nuna kawai ana amfanin da ita kadai ne a kasar India yanzu haka.
Ita dai wannan manhajar za ta nuna maka wani gargadi lokacin da motarka ta bar kan hanyar da kake tafiya.
Kamar yadda kamfanin Google ya bada zabin alamu, ya nuna karara cewa sakon sauka daga kan hanya an yi shi ne don ya zama manhajar tsaro, zai nuna maka alamun gargadi idan direban tasi da ya dauke ka zuwa inda kake son zuwa kai tsaye ba saboda wani dalili ba.
Facebook Forum