Kamfani Google da wasu manyan kamfanonin yanar gizo na sada zumunta suna kara fuskantar matsaloli wurin tantance bayanai da suke karba, daga masu amfani dasu. Google da Facebook wannan ne karon farko da suka fito da wadannan hanyoyi a cikin wannan shekarar.
Yanzu masu amfani da dandalin YouTube zasu iya tsara bayanan abubuwa da suka kalla, ko suka bincika a baya ta yanda zasu share kai tsaye ba tare da wani ya gani ba.
Shafin taswirar Google kuwa zai fara amfani da wata manhaja, wanda hakan ke nufin mai amfani da Google zai iya zirga-zairgar shi ba tare da an nadi bayanan wuraren da ya ziyarta ba. Za a samar da manhajar wadda za’a iya saukar da ita akan wayar android a cikin wannan wata. Sai dai Google bai yi karin bayani a kan ranar da za a fara saukar da manhaja a kan wayar iOS ta apple ba.