Kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets ta Najeriya ta fara gasar cin kofin duniya ta FIFA U-17 (kasa da skekara 17) na shekarar 2019 ta hanyar doke Hungary daci 4-2 a Brazil.
Gyorgy Komaromi ne ya fara zira kwallon farko wa Hungary mintuna uku da fara wasan, in da shi kuma Samson Tijani ya samarwa Najeriya bugun fanareti bayan mintuna 20.
Shi kuma Samuel Major ya sake zira wa Hungary kwallo a cikin minti na 28 inda ya su kungiyarsu akan gaba, kuma Usman Ibrahim ya zira wa Najeriya kwallo a minti na 79 a wasan inda ya mai da su dai-dai.
A minti na 82 ne, Oluwatimilehin Adeniyi ya zura wa Najeriya kwallon da ya sa kungiyar ta su kan gaba, kafin Samson Tijani ya karasa wasan, inda ya zira kwallo a minti na 87.
a yanzu dai, Najeriya za ta hadu da Ecuador a daren Talata.
Facebook Forum