A gobe Asabar In sha-allah shugabannin kasashen Afirka ta Yamma ke zaman taro na musamman domin nazartar halin da ake cimi a rikicin siyasar kasar Mali da kokarta tsara hanyar bi domin sake kwato yankin Arewaci daga hannun mayakan ‘yan tawayen Mali.
An gayyaci shugabannin Gwamnatin mulkin soji da shugabannin jam’iyyun siyasar Mali zuwa wajen wannan taron kolin shugababnmin ECOWAS da za’a gudanar a birnin Ouagadougou, kasar Burkina Faso.
Daretka janar na ayyukan hulda da kasa da kasa na ECOWAS, Abdel Fatau Musah yace babban batu dake ajandar taron kolin na gobe shine hanyar da za’a bi domin a fadada Gwamnatin rikon kwarya wadda karfin ikonta ke yankin kudanci domin hakan yasa ta sami kwarin gwiwar tinkarar matsalolin da suka shafi duk kasa kuma kowa ya amince da sahihancinta a Mali.