Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Fado Daga Jerin Kasashe 10 Mafi Girman Tattalin Arziki A Afirka


Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo

Ghana ta fado kasa daga jerin kasashe goma (10) mafiya karfin tattalin arzikin Afirka a wannan shekarar, wanda Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar yayin da Asusun ya yi hasashen habakar tattalin arzikin Ghana da kashi 2.8 cikin dari nan da ƙarshen 2024.

ACCRA, GHANA - Hakan ya bayyana ne a rahoton hasashen tattalin arzikin kasashen duniya na Asusun IMF.

Asusun Lamuni na IMF, ya yi amfani da ma’aunin tattalin arzikin kasa (GDP) daga dala biliyan 373 zuwa dala biliyan 79 na kasashen.

GDP na kasar Ghana a halin yanzu na kusan dala biliyan 75 ne, wanda hakan ya sa ta kasance kasa ta 11 mai karfin tattalin arziki a Afirka.

Haka kuma IMF a cikin rahoton ya yi hasashen cewa Ghana za ta samu karuwar kashi 2.8% a tattalin arzikinta zuwa karshen shekarar 2024, wanda ya yi kama da abin da gwamnatin kasar ta yi hasashe a cikin kasafin kudin 2024 da ta gabatar.

A cewar IMF, kasar Masar, wacce ke kan gaba a shekarar 2023, ana sa ran za ta koma matsayi na biyu a bayan Afirka ta Kudu, musamman saboda faduwar darajar kudin kasar.

Najeriya, wacce a da take kan gaba kuma aka yi wa lakabi da kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, ta koma matsayi na hudu a bana saboda irin wadannan dalilai.

Dukkanin kasashen biyu sun ga koma bayan tattalin arzikinsu sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudadensu.

Yunus Swalahudeen Wakpenjo, mai sharhi kan harkokin yau da kullum ya amince da hasashen IMF idan aka yi la’akari da mu’amalar asusun IMF da kasar Ghana, domin asusun na da jami’u a duk sassan tattalin arzikin Ghana.

"Kamar babban bankin kasa, ma’aikatar kudi, da wasu muhimman sassan tattalin arzikinmu suna wurin suna sai do kan yadda tattalin arkin kasarmu ya ce. Yanzu haka da muke magana, tarihin tattalin arzikinmu, tun daga hauhawar tsadar kaya, kudin ruwa na bankuna, da basussukan kasa da GDP, suna da labari’, a cewarsa.

Hamza Attijjany, mai sharhi kan tattalin arzikin kasa da harkokin kudi yace lallai akwai alamun cewa karfin tattalin arzikin Ghana zai sake dawowa domin kasar na bin hanyoyin gyara.

Yace, "Yawan hauhawar farashin kaya ya haura sama da kashi 50%, amma yanzu ya sauko kasa da kashi 30%. Darajar kudin Sidi (Cedi) ba ta faduwa kamar shekarar da ta gabata. Wadannan duka alamu ne cewa za a iya samun tattalin arziki Ghana zai yi kyau’.

Hamza Attijjany ya kara da cewa, idan Ghana ta bunkasa harkokin noma; ta yaki cin hanci da rashawa kuma ta rage yawan jami’un gwamnati da take kashe makudan kudade a kan su, kuma ta ci gaba da tabbatar da wasu shirye-shirye da ta kirkiro, kamar ‘Noma domin abinci da aikin yi’, da shirin ‘Gunduma daya dam daya’, tattalin arzikin Ghana za ta bunkasa.

Rahoton Asusun IMF ta ce, kasashen Afirka ta Kudu, Masar, Aljeriya, da Najeriya za su ci gaba da kasancewa kasashe hudu masu karfin tattalin arziki a Afirka har zuwa shekarar 2030.

A saurari cikakken rahoton Idris Abdullah:

Ghana Ta Fado Daga Jerin Kasashe 10 Mafi Girman Tattalin Arziki A Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG