WASHINGTON DC —
Fadar gwamnatin taraiyan Najeriya, ta nuna damuwata matuka dangane da sabobin bayane dake fitowa akan kudaden da suka bace a asusun ma'aikatan mai na NNPC.
Shugaban kasa Good luck Jonathan, yace ya amince cewa lallai dalar Amurka miliyan dubu goma sun salwanta daga asusun ma'aikatan NNPC.
Tun farko, gwamnar babban bankin Najeriya, wanda aka dakatar Sanusi Lamido Sanusi, yayi zargin cewa akwai makudan kudade da suka salwanta ganin cewa basu shiga asusun gwamnati ba.
A lokacin da shugaban kasa, yake ziyaran aiki a kasar Holland,ne ya furta haka sailin da yake ganawa dan 'yan Najeriya masauna kasar ta Holland.
Ya bada tabashi cewa lallai ana zargin wadanna kudade sun bata amma an fara daukan matakan na tabbatar da gaskiya al'amarin.