A Yau Laraba 10 ga watan Yulin shekara ta 2019 ne za'a fara wasannin daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka, wanda kasar Masar ta karbi bakonci sa.
Kasashe 8 ne zasu kece raini a tsakaninsu, karawar farko Senegal zasu fafata da Benin, da misalin karfe biyar na yamma a gogon Najeriya, Nijar, da Kamaru.
Sai kuma da karfe takwas za'a kece-raini tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu, wasan da ake ganin zai fi daukar hankalin 'yan kallo, shi ne tsakanin Najeriya da Bafana-Bafana na Afirka ta Kudu.
A tarihin haduwar kasashen biyu a manyan wasanni 12 da suka fafata, Najeriya ta yi nasara sau shida, ita kuwa Afirka ta Kudu sau biyu kadai tayi nasara, anyi kunnen doki sau hudu.
A fafatawarsu a baya-bayan nan a wasan neman tikitin shiga gasar ta cin kofin Afirka, Afirka ta Kudu ta doke Najeriya da ci 2-0 ranar 8 ga watan Yuni 2017 a gidan Najeriya.
Ita kuma Najeriya ta bita har gida su kayi kunnen doki 1-1 a ranar 17 ga watan Nuwambar 2018. A ranar Alhamis kuwa kasar Ivory Coast zata kara da Aljeriya sai kuma Madagascar da Tunisiya.
Facebook Forum