WASHINGTON D.C. —
Yayain da kungiyar wasan kwallon fafar Kamaru ke kokarin kare hare-haren da ake kai musu, Canada ta samu damar zura kwallo daya da take bukata akan Kamarun.
Amma Argentina ta hana Japan katabus inda ta samu maki na farko tunda take buga gasar cin kofin duniya na mata.
A birnin Paris, Argentina ta hana Japan taka leda yadda ya kamata, kungiyar da taje wasan karshe har sau biyu, da ta kai wasu munanan hare hare har guda uku ba tare da samun damar zura kollo ba har aka kammala wasan, da aka tashi an yi canjaro 0-0, wanda a gasar kuma shine na bakwai a tarihin.
Sakamakon ya bar duka kungiyoyin da maki daya-daya a rukunin D, da suke bayan Ingila da ta lallasa Scotlan a ranar Lahadi.
Facebook Forum