Kocin tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Gareth Southgate ya ce za su shigar da kara a gaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai kan batun nuna wariyar launin fata.
Southgate yace, ba za a amince da irin wannan dabi’ar ba, ya kuma jaddada cewa, da kunnensa, ya ji ana zagin dan wasansa Danny Rose, a wasan da Ingilar ta lallasa Montenegro da ci 5-1 a gasar neman tikitin shiga gasar cin kofin kasashen Turai na shekarar 2020.
A lokacin wasan na ranar Litinin, da ta gabata an yi ta rera wake wake na nuna wariyar launin fata da muzanta wa ga wasu daga cikin 'yan wasa.
A bangaren guda kuwa Hudson Odoi ya ce, shima yaji da kunnesa, magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Montenegro na kukan birrai, don nuna wariyar ta launin fata inda yace sam haka bai kamata a rika samun irin
wannan dabi’ar ba.
A wasan dai Montenegro ita ta fara jefa kwallo a ragar Ingila cikin mintuna 17, ta kafar dan wasanta Vesovic kafunnan dan wasan Ingila Ross Barkley, ya rama mata a mintuna 30:39 da kuma mintuna 59 inda yaci kwallaye uku, Harry Edward Kane da Raheem Sterling kowannensu ya jefa kwallo daya.
Facebook Forum