Rana mai kamar ta yau Juma'a 9 ga watan fabrairun shekarar 1990 ne wasu daibai uku suka rasa rayukansu sanadiyar arangamar da suka yi da jami'an tsaron Yamai, yayin da suke zanga-zanga akan halin da jami'arsu take ciki.
Hakan ce tasa a kowace ranar 09 ga watan Fabrairun kowace shekara ilahirin daliban Jami'ar Abdulmumuni da sauran daliban makarantun birnin Yamai su kan yi gangamin tunawa da 'yan uwan nasu da suka kwanta dama.
A wannan shekarar ma bata canza zani ba saboda daliban Jami'ar Abdulmumunin da duk makarantun Yamai sun fito yin wannan gangamin da suka saba. Mataimakin Sakataren daliban Jami'ar birnin Yamai Tsalha Tela, yace a irin wannan ranar ce a shekarar 1990 abokan nasu suka fito suna jerin gwano amma jami'an tsaro suka hallakasu.
Shekaru 28 bayan kisan har yanzu radadin kisan na ci gaba da haddasa juyayi a cikin dalibai inji Abdu Shehu Musa, dalibi a Jami'ar Abdulmummuni ta Yamai. Yace ko da yake abin ya faru lokacin ma ba'a haifesu ba, amma idan mutum ya ji tarihin faruwar lamarin sai ya zama tamkar yau aka yi abin.
Ya yi kira mahukuntan Nijar da su kwato masu hakkinsu ta kamawa da hukunta wadanda suke da hannu a mutuwar 'yan uwan nasu. Duk gwamnatin data kama mulki a Nijar ta kan fuskanci matsin lamba daga kungiyar dalibai akan wannan lamari, saboda suna so a gano wadanda suka yi aika-aikar tare da hukuntasu.
Ga muryar cikakken rahoton Sule Mumuni Barma daga kasa.
Facebook Forum