Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gamayyar su sabon Shugaban Senegal ta yi gagarumin nasara


Sabon Shugaban Senegal Macky Sall
Sabon Shugaban Senegal Macky Sall

Sakamakon farko-farko na zaben ‘yan Majalisar Senegal da aka gudanar ranar Lahadi na nuna cewa gamayyar da sabon zababben Shugaban Senegal Macky Sall ke shugabanta ta yi gagarumar nasara.

Sakamakon farko-farko na zaben ‘yan Majalisar Senegal da aka gudanar ranar Lahadi na nuna cewa gamayyar da sabon zababben Shugaban Senegal Macky Sall ke shugabanta ta yi gagarumar nasara.

Hukumar Zaben Kasar ta sanar da sakamakon wuccin gadi a jiya Laraba, inda ta ce Gamayyar Bokk Yakaar ta su Shugaba Sall ta ci kujeru 119 a Majalisar mai jimlar kujeru 150.

Shugaban Hukumar Zaben kasar Demba Kandji, ya ce jam’iyyar Senegalese Democratic Party (PDS) da ada ke shugabantar kasar ta sami kujeru 12, wani rukunin jam’iyyar ta PDS da ya balle kuma ya sami kujeru 5, a sa’ilinda sauran kananan jam’iyyu kuma su ka sami kujeru 15.

Ba a fito zaben ba sosai. Da kadan ma wadanda su ka fito zaben su ka dara 1/3 na mutane miliyan 5 da su ka yi rajistar yin zabe.

Nasarar ta gamayyar su Mr. Sall za ta sa sabon Shugaban ya iya jaddada batun garanbawul a fannin tattalin arziki don ya iya cika alkawarinsa na lokacin zabe na rage yawan rashin ayyukan yi tare da rage fatara a kasar.

XS
SM
MD
LG