WASHINGTON, DC —
Yawan yiwa mata fyade a jahar Katsina ya sa Majalisar dokokin jahar ta zartas da kudirin dokar hukunta masu aikata wannan danyen aiki. Shirin dokar yayi tanadin hukuncin daurin rai da rai, ko dauri mafi sauki na shekaru goma sha hudu da biyan tarar Nera dubu hamsin da kuma biyan diyya a kan duk wanda aka samu da aikata fyade a jahar Katsina. Wanda ya gabatar da kudirin dokar a zauren Majalisar shi ne Alhaji Rabiu Idris mai wakkiltar mazabar Funtua, wanda ya ce wannan doka da ma akwai ta, yanzu kawai gyara aka yi. A tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna, Alhaji Rabiu Idris yayi karin bayani sosai akan shirin dokar, kuma ya ce hatta 'yan luwadi da 'yan madigon jahar Katsina akwai hukuncin da dokar ta tanadar mu su:
Alhaji Rabiu Idris daga mazabar Funtua ya ce dokar za ta rafki duk wanda aka samu ya yiwa mace fyade, ko karamar yarinya ce ko babba ce ko ma wacece