Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fulani Sun Koka kan Halin Da Suke Ciki


Shanun Fulani
Shanun Fulani

Fulani a jihohin da aka fara anfani da dokar hana kiwo barkatai sun koka akan irin halin da suke ciki, sun bukaci gwamnatin tarayya tayi wani abu akai.

Yanzu haka, dokar hana kiwo da wasu jihohi a arewacin Najeriya suka soma aiwatarwa,ya soma jefa makiyaya da dabbobin su cikin wani mawuyacin hali da ka iya shafan tattalin arziki.

Kama daga jihar Binuwai, Nasarawa zuwa Taraba da Adamawa kawo yanzu akwai daruruwan Fulani makiyayan da ke cikin mawuyacin hali sakamakon tashe tashen hankulan dake faruwa.

Wasu makiyayan cewa suke dabbobinsu na mutuwa sabili da kona wuraren kiwon da aka yi musamman a jihar Binuwai da Taraba inda aka soma aiwatar da dokar hana kiwo,kamar yadda wannan makiyayin ya shaidawa wakilin Muryan Amurka Ibrahim Abdulazeez

Kungiyarta makiyaya tace muddin gwamnati bata tashi tsaye ba,to fa labudda kasar ka iya fadawa wani halin tashin hankali da kuma tattalin arziki.

Dr Aliyu Tilde na kungiyar Fulbe Global wanda da shi aka zaga wasu wuraren da lamarin ya shafa musamman a jahar Banuwai,ya bayyana abun da suka gani da kuma halin da ake ciki.

Ga Ibrahim Abdulazeez da Karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG