Makonni shida da suka gabata aka rufe filin jirgin sama na Abuja, saboda yin gyara da alkawarin kammala ayyukan cikin makonni shida.
Yayinda ake rufe filin Ministan Zirga Zirgan Jiragen Sama na Najeriya Hadi Sirika yace ba zasu wuje ranar 19 ga wannan watan Afirilu ba da zasu sake bude filin bayan an kammala ayyukan gyara da za'a yi.
Amma cikin ikon Allah kwana daya kafin ranar da ministan ya bayar sai jirgin Ethiopia ya sauka a filin wanda ya tabbatar da kammala ayyukan gyara tare da sake bude filin.
Inji Minista Sirika an yi gyare gyaren da suka dace na hanyar tashi da saukan jiragen kuma ba zai rika tara ruwan sama ba kamar da.
Jami'ai na bangarori daban daban da suka koma Kaduna da ayyukansu an basu umurnin dawowa domin sake bude ofisoshinsu a tashar. Wasu ma tun jiya Litinin 17 ga wata suka fara hakan. Tun farko ma an umurci hukumomin gwamnati dake aiki a tashar da su bude ofisoshinsu jiya Litinin
Kwamandan hukumar dake yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi na Abuja Hamisu Lawal ya kama hanyar komawa filin jirgin domin kama aiki gadan gadan.
Gwamnati ta ware Naira biliyan biyar da miliyan dari takwas domin aikin.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum