Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce zata dakatar da Najeriya daga shiga duk wata gasa ta kasa da kasa idan har gwamnati ba ta soke shirinta na haramta kungiyar kwallon kafar kasar, Super Eagles, na tsawon shekaru biyu kamar yadda ta ce ba.
Gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, wadda ta ce zata soke kungiyar saboda kunyar da ta bayar a gasar cin kofin duniya a Afirka ta Kudu, ta kuma ce zata rushe Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya ta maye gurbinta da wata hukumar ta wucin-gadi.
Hukumar FIFA ta ce ta fadawa shugaban Najeriya cewa ta ba shi wa’adin zuwa karfe 5 na yammacin ranar litinin (agogon Najeriya), 5 ga watan Yuli, da ya soke haramcin da yayi ma kungiyar ta Super Eagles. Har ila yau ta ce hukumar ta FIFA ba zata amince da duk wata hukumar gudanar da kwallon kafar da gwamnati zata kirkiro ba.
Idan har FIFA ta dakatar da kasar, to zata dakatar da dukkan agajin kudi da ta ke ba Najeriya, sannan zata haramtawa kungiyoyi da kulob-kulob na kasar shiga duk wata gasa ta kasa da kasa.